Kalubale

A takaice: Lafiyar alumma, ingancin rayuwa da kuma samun abubauwan more rayuwa ya dogara ne ga kokarin su na taimakawa juna ta hanyar samar da abinci mai gina jiki da sauran abubuwan bukatu na abincin yau da kullum. Gimshikan abubauwan da zasu samar da abincin (mutane, kudi, ma’adinai da sauransu) sunyi karanci kwarai.

Misalai

Samun abinci ta hanyar kara yawan abinda ake nomawa da kuma kawo hanyar dogaro da kai yayin noma abincin.

 • Shin akwai yadda za’a iya samar da noman rani a saukake?
 • Ya za’a magance lalcewar anfanin gona bayan girbi ta hanyar kyautata adani?
 • Akawai hanyoyin rage asara dalilin ambaliyar ruwa.

Karancin hanyoyi da kuma taimako daga waje na samar da abinci

Karancin noma, su (kamun kifi) da kuma kiwon kanana da manyan dabbobi

Samun takin zamani cikin farashi mai sauki da kuma maganin kwari da ciyawa

 

 

Fadada hanyoyin samar da abinci

Karancin hanyoyin kudi, kasuwanni, ababen more rayuwa da kuma sanao’in hannu

Misalai

 • Shin akwai hanyar da za’a samar da horo na sanao’in hannu domin fadada hanyoyin abinci?
 • Ana iya samun sababbin fasahohi na fadada hanyoyin abinci tare da kuma kara ma abincin da ake samarwa inganci?
 • Zai yiwu a samar da makamashi wanda bai dogara da gwamnatin tarayya ba domin saukake ayyukan abinci a mataki na gidaje.

 

A takaice: Sansanin yan gudun hijira sun yi karanci. Wannan ya haifar da karancin abubuwan more rayuwa a sansanin. Bugu da kari, abubuwan bukatu na yau da kullum suna lalcewa a yayin da turmutsutu yana kara kamari.

Misalai

 • Shin ana iya samun hanyoyin gyaran mazaunai kokuma bada kwarin guiwa ga mazuna domin gyaran mazaunan?
 • Akwai hanyoyi da za’a iya mangance rashin muhalli da kuma kayan karatu ga yan gudun hijira da kuma mutan gari?
 • Akwai tsammanin cewa kimiyyoyi wadanda ba na gwamnati ba, kamar wutar lantarki mai amfani da rana, naurar sanyaya wuri da tsaftar muhalli zasu taimaka a sansanin yan gudun hijira?
A takaice: Karancin wuraren karatu a cikin kwanciyar hankali, ko kuma karancin abubuwan koyarwa a kauyakku da dama. Haka kuma yara basu samun karatu mai nagarta. Iyayen yara basu ganin muhimmancin karo karatu, bayan yaran sun gama makarantun sakandere. Wannan yana faruwa a lokutta da dama.

Misalai

 • Shin akwai hanyoyin samar da abubuwan koyarwa na zamani dabn-daban ga dukkan makarantun yanki ko gunduma?
 • Wadanne irin tsare-tsaren koyarwa ne masu alaka da sanao’in hannu, zasu habbaka fahimtar karatu ga dalibai na makarantun sakadere da kuma na gaba da sakandere? Ta yaya za’a yi anfani dasu domin cimma wannan bukatun?
 • Akwai hanyoyi masu dorewa na rage tsadar littafan makaranta da kuma bada tallafi domin cigaba da karatu  (kamar samar da kadarori masu samar da kudi)?
 • Ana iya samar da karuwar hanyoyin karatu mai ma’ana tare da amfani da naurar gizo-gizo?
 • Ta ya za’a iya kyautata abubauwan more rayuwa a makarantu tare da taimakon alummar yanki?
A takaice: Tsananin karuwar mutuwar mata masu ciki da kuma kananan yara

Karancin kula da lafiyar masu ciki, fadakarwa kan kiwon lafiya, rashin kudi da kuma kyakkyawar kula da lafiyar masu ciki da kananan yara yana haifar da tsananin kalubale ga alummar

Misalai

Akawi dabaru ko tsare-tsare wadanda zasu samar da kiwon lafiya ga mata masu ciki; kafin, a yayin daukar cikin da kuma bayan haihuwa; ta hanyar samar da abinci mai nagarta da muhalli mai tsafta?

Akwai tsare-tsare masu tasiri na wayar da kai ga iyalai da masu juna biyu akan kula da lafiya, abinci mai gina jiki da kuma kula da yara?

Akwai sababbin tsare-tsare ko kimiyya wandanda za su bada damar samun cin gajiyar kula da lafiya ko samun lura da masu juna biyu?

Akwai hanyoyin samar da ababen hawa da kudade ga iyayen yara da masu juna biyu domin samun saukin zuwa asibiti musamman lokacin da ake bukatar agajin gaggawa?

Ya za’a magance mtsalolin abinci mai gina jiki da kuma magance ciwarwata na yau da kullum kafin daukar ciki, yayin daukar ciki da kuma bayan haihuwa?

Karancin samun saduwa da alummomi da suke a wuraren da tsaro ya karanta

Karancin samun adalci a wurin shariah da kuma tsaron rayuwa